So da dama mutane suna fuskantar matsaloli yayin da suke chaja wayoyin su na android.
Shine na rashin saurin chaji to kuma mutane suna nuna rashin Jin dadin su akan wannan matsalar.
Wannan na faruwa ne saboda mafiyawancin android din da Ake kerawa a wannan zamani ana yin su da batiri Mai karfin gaske shi yasa kananun chajoji basa iya chaza su.
To ga Wani application da zai taimaka maku domin chaza wayoyin ku cikin sauri,Mai suna "fast charger pro".
Misali:idan wayar ka tana yin awa 3 kafin ta cika, to wannan Application din zai taimaka mata domin ta cika acikin awa 1.5
Amma ka lura:shi wannan Application din yana aiki a wasu wayoyin, sannan baya aiki a wasu wayoyin.
Saboda haka sai kayi Downloading din domin ka gwada ka gani idan yayi a wayarka ta Android.
Sannan shi wannan application din yana aiki ne a wayoyin Android kadai.
