Yadda zaka canzawa Sim card dinka network operator(service provider).

📱 Yadda Zaka Canza Network Operator Ba Tare da Ka Canza Lambar Waya ba (MNP)

🧐 Menene MNP?

MNP (Mobile Number Portability) wata dama ce da gwamnatin Nigeria ta kawo tun shekarar2013. Wannan tsarin yana ba ka ikon canza network operator (service provider) zuwa wani operator (misali daga MTN zuwa Airtel, ko daga Airtel zuwa Glo), amma ka ci gaba da amfani da lambar waya ka da kowa ya riga ya san ka da ita.


✅ Abubuwan Da Kake Bukata Kafin Ka Fara

  • SIM dinka wanda yake a active
  • Ka tabbatar Lambar ka an hada ta da NIN din ka
  • Ka je ofishin network din da kake so kayi migrating (MTN, Airtel, Glo, 9mobile)
  • Ana bukatar ID Card (NIN card/slip, Driver’s Licence, ko Voter’s Card)

🛠️ Matakan Da Zaka Bi

  1. Ziyarci ofishin network din da kake so ka canza layin,Misali: Idan kana so ka sauya daga MTN zuwa Airtel, sai ka je ofishin Airtel.
  2. Cika fom (MNP Form): Za a baka fom inda zaka saka sunanka, lambar ka, da bayanan ID dinka.
  3. zasu bukaci ka aika da sakon “PORT” zuwa 3232: a tsohon sim card din ka saboda su tabbatar da cewa kai kake son canjin.
  4. Zasu baka sabon SIM: Sabon SIM din wanda ke dauke da lambar ka ta da amma a sabon network.
  5. Jira canjin ya kammala (24–48 hours): A lokacin tsohon SIM dinka zai daina aiki kafin sabon din ya fara aiki.

⚠️ Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata ka sani a MNP

  • Ba zaka iya sake canza network zuwa wani network ba sai bayan kwanaki 90 (wata uku).
  • Airtime da ke kan tsohon SIM dinka ba zasu koma zuwa sabon network ba, don haka ka kashe kudin ka kafin kayi canjin.
  • Bayan ka gama, lambar ka zata ci gaba da aiki kamar yadda aka saba – ba wanda zai gane ka sauya network saidai in kai ka fadama wani.

🌟 Amfanin MNP

  • Zabin network mafi kyau ba tare da rasa lambar ka ba
  • karin ’yanci wajen amfani da sabis na kamfanoni
  • Kare kanka daga siyan sabbin layuka da sanar da abokai

🔗 Wannan bayani zai taimaka maka wajen fahimtar yadda zaka sauya network dinka cikin sauki, ba tare da wahala ko rasa lambarka ba.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post

Advertisement

Advertisement