A wasu yan shekaru da suka wuce kafin in fara samun kudi a internet,ina mamakin mutanen dake fada cewa wai ta yanar gizo suke samun kudi,har sai takai cewa zuciya ta na karyata wadanan mutane a duk sa'ar da suka yi irin wannan magana.
Amma bayan na fara aiki a timebucks, wannan shakku ya kau.
Na samu kudi da timebucks sosai wanda ban san iya adadin su ba.
Menene TimeBucks?
TimeBucks shafi ne na dake samar da damarmaki na samun kuɗi a intanet wanda ke bawa masu amfani damar yin ayyuka daban-daban domin su sami rewards. Wannan shafi an samar da shi ne tun daga shekarar 2014, kuma yana da izini, kuma har yanzu yana biyan kuɗi ga mutanen dake aiki dashi.
A TimeBucks, za ka iya samun kuɗi ta hanyar:
*Cike tambayoyi (Surveys)
*Kallon bidiyo
*Danna tallace-tallace (PTC Ads)
*Yin rajista a wasu shafuka
*Gwada sabbin manhajoji (Apps)
*Yin bayani akan shafin internet
* Gayyatar mutane (Referrals)
TimeBucks na bawa mutane daman samun kuɗi ba tare da saka ko sisin kwabo ba. Wannan yasa ya zama daya daga cikin shafukan da suka fi shahara a duniya wajen samun kuɗi a intanet.
Yadda Ake Rijista a TimeBucks
Domin fara samun kuɗi a TimeBucks, sai ka bi waɗannan matakai:
* Shiga shafin TimeBucks – ta hanyar wannan link din:
https://timebucks.com/?refID=222297458
* Danna "Sign Up"
* Cika bayananka kamar suna, imel, da kalmar sirri
* Tabbatar da Imel daga akwatin saƙonka
* Shiga cikin asusunka domin fara aiki
Bayan ka gama rijista, za ka iya fara samun kuɗi kai tsaye.
Hanyoyin Samun Kuɗi a TimeBucks
1. Cike Tambayoyi (Surveys)
Kamfanoni suna buƙatar ra’ayoyin mutane game da samfuran su, don haka suna biyan kuɗi ga masu amsa tambayoyi (surveys).Za ka iya samun $0.50 zuwa $3 a kowanne survey , amma ya danganta da tsawon sa da kuma ƙasarka.
2. Kallon Bidiyo
Za ka iya samun kuɗi ta hanyar kallon bidiyoyin talla ko wasu bidiyoyi na musamman.
Kowanne bidiyo yana da tsawon lokaci, kuma sai ka kammala kallonsa kafin a biya ka.
Za ka iya samun $0.01 zuwa $0.10 kan kowanne bidiyo.
3. Danna Tallace-tallace (Click Ads - PTC Ads)
Akwai tallace-tallace da ake buƙatar ka danna su sannan ka duba na ƴan dakiku kafin a biya ka.
Wannan hanya ce mai sauƙi, amma yawan kuɗin da ake bayarwa gaskiya ba su da yawa.
Ana iya samun $0.001 zuwa $0.02 kan kowanne talla.
4. Yin Rajista a Wasu Shafuka (Signup Offers)
Idan ka yi rajista a wasu shafuka ko ka gwada wasu apps, za ka iya samun reward.
Wasu shafuka na bukatar ka yi amfani da su na wani lokaci kafin a biya ka.
Za ka iya samun $0.50 zuwa $5 a kowacce rajista.
5. Aikin Social Media
Za ka iya samun kuɗi ta hanyar yin ‘Like’, ‘Follow’, ko ‘Subscribe’ a shafukan sada zumunta kamar Facebook, Instagram, YouTube, da sauransu.
Ana iya samun $0.01 zuwa $0.10 a kowanne aikin social media.
6. Tsarin Referral (Gayyatar Mutane)
Idan ka gayyato mutane su shiga TimeBucks ta hanyar link ɗinka, za ka sami kaso daga cikin abin da suka samu.
Wannan hanya ce mai kyau don samun kuɗi idan kana da mutane da za su yi rajista ta hanyar link ɗinka.
Za ka iya samun har 10% daga abin da mutanen da ka gayyata suka samu.
7. Yin amfani da shafin ka na internet domin yin bayani akan timebucks.
Idan kana da blog ko shafi a kafar sada zumunta, za ka iya rubuta bayani ko ƙirƙirar bidiyo game da TimeBucks ta hanyar saka referral Link din ka sannan ka sami reward.
Bayan ka tara kuɗi a asusunka, wanda anason a kalla sukai $5 ,za ka iya cire su ta hanyoyi kamar:
1-PayPal
2- Bitcoin (amma a yanzu sun dakatar da withdraw da Bitcoin)
3-Skrill
4-Bank Transfer (ga wasu ƙasashe)
5- AirTM
6-litecoin
Yadda zaka yi domin samun Kuɗi Mai Yawa a TimeBucks
*Yi aiki kullum – Ka duba shafinka akai-akai don samun sabbin ayyuka.
*Yin Survey – Wannan ita ce hanya mafi sauri ta samun kuɗi a TimeBucks.
*Yi amfani da tsarin gayyata (Referrals) – Idan ka gayyato mutane da yawa, za ka samu kuɗi daga abin da suke samu.
*Ka duba sabbin (Offers) – Wasu offers na bayar da rewards mai yawa fiye da wasu.
*Ka yi amfani da hanyoyi da dama – Kada ka dogara da hanya guda ɗaya kawai,misali kada kace survey kadai zaka cigaba da yi .
*Yin tasks – zaka iya yin tasks domin abiya ka
Da gaske ne timebucks ingantacce ne?
TimeBucks yana da cikakken inganci kuma ana samun kudi sosai dashi. Yana da cikakken izini, kuma mutane da dama har da ni kai na sun tabbatar da ana samun kuɗi matuka da shi.
