Yan uwa barkan mu da warhaka barkan da sake saduwa sannan Kuma Muna sallama: Assalamualaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Yauma gamu dauke da Wani bayani Wanda zai amfanar daku.
Bayani
A yan kwanakin nan, kamfanin Layin aitel suna sangarta abokan huldar da su, ta hanyar basu wata garabasa in suka saka kudi yan kadan. Tabbas airtel kamfani ne dake kula da abokan huldar su matuka.
Daga bayan wani lokaci zuwa lokaci kamfanin airtel suna gwangwaje abokan hudar su da katin kira ko datar shiga shafin yanar gizo domin jin dadin abokan huldar tasu. Kamar yadda suka saba wannan Karon ma sun kawo wani tsari da zai farantawa abokan huldar su, ta hanyar amfani da tsarin USSD.
Zaka iya samun 1.5GB akan N300 kacal, da kuma 5GB akan N1000 kacal, ko sama da haka, ya danganta da yayin yadda kake saka kati da kuma dadewar Layin naka.
Saboda haka kan phone dialer naka ka kira *141*1# domin ko ka cacanta da tsarin.
Muna godiya.

