Barkan mu da warhaka , yauma gamu da Wani bayanin na bonus a layin MTN.
Bayani game da bunos din na layin mtn
Mtn special airtel data, tsari ne dake ba abokan hulda damar samun garabasa mai yawa ta hanyar saka
wasu kalilan din kudi.
Zaka amfana da wannan tsarin idan kana amfani da Layin MTN kuma ana nigeria wannan garabasar yake aiki, bansan sauran kasashe ba, amma zaka iya gwadawa ka duba ka idan yana aiki a Kasar ka, idan kana aiki ne a wajen nigeria.
Dukkan wanda yake cikin na nigeria zai iya amfana da wannan tsarin, in har kana da Layin MTN.
Sannan ka lura da cewa kowane abokin huldar yana da irin ta sa garabasar,abin nufi garabasar da suka ba wani abokin huldar na su ya sha bamban da yadda za su ba wani.
Misali:idan suka ce ka saka N100 su baka N200, to wani za su iya cewa ya saka N400 ya samu N800 ya danganta da yadda ka dade ka amfani da Layin.
Kuma zaka iya samun Data na shiga Internet ko kudin kira ko kuma duka.
Danna *121# domin tsarin da ya dace da ku.
MTN - EVERY WHERE YOU GO.
