Call forwarding wani tsari ne da duk wayoyin salula suke zuwa da shi. Yana bada damar karkatar da kira zuwa wani Layin, zaka iya karkatar da kiran wayar ka zuwa sim card din kake so, sannan kuma zaka iya amfani da shi domin dakatar da dukkan kiran da a keyi maka a Layin ka.
Bi wadannan matakan domin ka saka ko fitar da call forwarding.
Farko kaje zuwa phone dialer na wayar ka, sai kayi click na wasu digagga guda uku da Saman gefen screen din wayar ka a hannun dama.
Sai ka nemi inda aka rubuta Settings sai kayi click.
Bayan ka yi click, sai ka nemi inda aka rubuta Calling Account sai ka yi click.
Sai ka zabi sim din da kake so ka saka call forwarding din.
Sai ka danna inda aka rubuta Call fowarding,
Zaka abubuwa kamar haka:
Always forward
When busy
When unanswered
When unreachable.
Dukkan su zaka same su a off ne idan ba a saka fowarding din ba kenan.
Sai ka zabi wanda kake so ka saka. Idan kuma kana so ka fitar da forwarding, wadannan dai matakan zaka bi har a kawo wajen wadannan matakan saika duba wanda yake a On, sai kayi click din shi sa'annan ka kashe shi.
Wannan shi ne hanyar da zaka bi domin ka saka ko fitar da call forwarding a wayar Android.





