Dalilin da ya sanya darajar naira ta farfado

 
 

 
 Darajar kuɗin Najeriya ta naira ta ɗan farfaɗo da kashi 16.3 cikin 100 a kwana uku idan aka kwatanta da faɗuwar da ta dinga yi da kashi 36.52 cikin 100 a shekarar 2022.
 
 
 
 'Yan kasuwar canji a Kano sun faɗa wa wakilin mu cewa kasuwar canji ta bayan-fage ta tashi a ranar Alhamis ana canzar da dalar Amurka ɗaya tsakanin N750 zuwa N760 a Kano.
 
 
 
 A makon da ya gabata, an canzar da dala ɗaya kan N890 a kasuwar da ba ta hukuma ba, yayin da farashin bai wuce N439 ba a farashin gwamnati.
 
 
 Sai dai ana danganta farfaɗowar nairar da ƙarancinta da aka fara fuskanta a kasuwar canjin sakamakon wa'adin da CBN ya bayar na soke amfani da tsofaffin takardun naira na N200 da N500 da N1,000 na ƙaratowa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post

Advertisement

Advertisement