@Qatar-world_cup_202: Japan ta lallasa kasar Germany a gasar cin kofin kallon kafa ta duniya Wanda ake gudanarwa a kasar Qatar.
Bayan ta zura Mata kwallaye har 2. Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci
Germany ta zura kwallo aragar Japan. Saidai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Germany ta kwashi kashin ta a hannu, bayan da Japan ta rama kwallon .
A mintuna na 73 Japan ta sake zura Kwallo ta biyu a ragar Germany wanda hakan ya ba Japan nasara akan Germany da ci 2-1.
